Sports
Kano Pillars Ta Sallami Sabon Mai Horos Da Kungiyar Wanda Ta Dauka Kasa Da Wata Guda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sabon shugabancin hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya sanar da soke kwantaragin Paul Offor a matsayin mai horar da kungiyar.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sashen yada labarai na hukumar gudanarwar kungiyar ya fitar, yace an soke kwantaragin Paul ne bisa fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.
Rahotanni na nuni da cewa kasa da wata guda, tsohon shugaban kungiyar ta Kano Pillars Alhaji Babangida Umar Little ya nada Paul Offor mai horar da Kungiyar.
Sai dai tuni sabon shugaban kungiyar ya sanar da soke kwantaragin Paul din yayi da kingiyar ke tunkarar kakar wasannin shekarar 2024/2025 da ake shirin farawa a wata mai kamawa