Connect with us

News

Hukumar INEC Ta Musanta Zargin Siyar Da Katin Zabe Na dindindin PVC

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta karyata rahoton da aka yi ta yada cewa jami’anta na sayar da katunan zabe na dindindin, PVC, gabanin zaben gwamnan jihar Edo da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Advertisement

Ya yin da ta bayyana zargin a matsayin karya, INEC ta kalubalanci wata kungiyar jama’a mai suna Transparency for Electoral Systems Advocacy, TESA, da ta bayar da kwararan hujjoji kan jami’an zabe domin tabbatar da ikirarinta na sayar da PVC a Edo.

Jerin Sunayen Jami’o’i 8 Na Kasar Benin Da Togo Gwamnatin Tarayya Da Ta Amince Da Nagartar Su

Babban Sakataren Yada Labarai na Shugaban Hukumar ta INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ne ya bayyana hakan ya yin da yake mayar da martani ga zargin.

Advertisement

Ya ce Hukumar ba ta sayarwa amma tana bayar da PVC kyauta ga masu rajista kawai.

A cewarsa, wannan zargin ya biyo bayan irin labaran da kungiyoyin ‘yan banga ke yi wa Hukumar a duk lokacin da ake shirin gudanar da zaben gwamna ko kuma babban zabe.

Advertisement

Ya kara da cewa da bullo da tsarin tantance masu kada kuri’a na Bimodal BVAS, ya zama abu mai wuya ga wani mai kada kuri’a ya yi amfani da PVC na wani don kada kuri’a.

Oyekanmi ya ci gaba da cewa, duk wani PVC da ba karba ba, ba za a iya amfani da shi wajen kada kuri’a a lokacin zaben Gwamnan Jihar Edo ba, yana mai jaddada cewa duk wanda ya yi yunkurin yin hakan za a kama shi a mika shi ga jami’an tsaro a ranar zabe.

Advertisement

“Bayan haka, an fara aikin karbar PVC ne kawai a mazabu 192 da ke Jihar a ranar Alhamis 22 ga watan Agusta kuma za a kare a yau Litinin 26 ga watan Agusta. Bayan haka, tarin PVCs zai motsa zuwa ofisoshin kananan hukumomin mu 18 daga 28 ga watan Agusta zuwa 8 ga watan Satumba 2024.

“Saboda haka, duk ‘PVCs da ba a karba ba’ ba zai iya isa ba lokacin da, a gaskiya, an fara aikin karba.

Advertisement

“Duk da haka, muna karfafa TESA da sauran mutane da ke da kwararan hujjoji na aikata rashin da’a a kan kowanne jami’in zaben mu da su gaggauta ba wa hukumar shaidar don daukar matakin gaggawa,” Oyekanmi ya kara da cewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending