News
Najeriya, Azerbaijan, Kazakhstan, Gabon, Na Daga Cikin Ƙasashen Da Ke Sayar Wa Isra’ila Ɗanyen Mai Da Fetur – Bincike
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An bayyana cewa Najeriya na cikin ƙasashen hukuncin aikata laifin kisan-gilla a yaƙin Gaza zai rataya a wuyan su, saboda bincike ya gano yadda ƙasashen ke sayar wa Isra’ila da fetur da ɗanyen mai yayin da ta ke ci gaba da yaƙin Gaza.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa wasu ƙwararrun masana shari’ar ƙasa da ƙasa da laifukan yaƙi, sun gargaɗi Najeriya da sauran ƙasashen masu hannu dumu-dumu wajen sayar wa Isra’ila mai cewa sun fa karya Yarjejeniyar Taron Geneva kan Laifukan Kisan-gilla.
Hukumar INEC Ta Musanta Zargin Siyar Da Katin Zabe Na dindindin PVC
An yi wannan taron yarjejeniyar a ranar 26 ga Janaidu, kuma Najeriya da sauran ƙasashe masu hannu a sayar wa Isra’ila ɗanyen mai da fetur duk su na ciki, sun kuma da hannun amincewa da hukuncin da ka iya biyo bayan waɗanda suka taimaka wajen yi wa fararen hula kisan-gilla a lokacin yaƙin Isra’ila da Falasɗinawa.
Babbar Kotun Ƙasa da Ƙasa ta Duniya (ICJ) ce ta rattaba dokar a Geneva, dangane da masu taimaka wa Isra’ila kan yaƙin Gaza.
Sai dai kuma bayan yin wannan hukunci tankokin Isra’ila da jiragen yaƙi da motocin sojojin su har ma da motocin rusau ɗin gidajen sun ci gaba da hare-hare a Gaza kan gidajen Falasɗinawa.
Wata ƙungiyar jinƙai ta Oil Change International (OCI) ce ta gudanar da binciken, inda ta bankaɗo ƙasashe irin su Najeriya sun rufe ido, sun ci gaba da sayar wa Isra’ila ɗanyen mai, gas da fetur waɗanda take shayar da jiragen yaƙi, tankokin yaƙi, motocin ɗaukar sojoji da motocin rusau, su na kutsawa Gaza da yankin West Bank su na rugurguza gidajen fararen hula.
Binciken ya gano cewa tsakanin ranar 21 ga Oktoba zuwa 2023 zuwa 12 ga Yuli 2024, Najeriya da sauran ƙasashen da ake zargi sun loda manyan tankokin jiragen ruwa maƙare da mai har jiragen ruwa 65 zuwa Isra’ila.
Sauran ƙasashen baya ga Najeriya sun haɗa da Azerbaijan, Kazakhstan, Gabon, Brazil da kuma Congo wadda ita kwanan nan ta shiga sahun su, sai kuma ƙasar Italiya, duk su ne manyan masu shayar da jiragen yaƙi da motocin yaƙin Isra’ila fetur da ɗanyen mai da gas.
Binciken ya tabbatar da cewa sun sayar wa Isra’ila tan miliyan 4.1 na ɗanyen mai, kuma fiye da rabin wannan mai an sayar da shi ne bayan Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICJ) ta yi hukuncin da ya haramta wannan cinikin.
Sai kuma ƙasar Amurka wadda ta riƙa aika fetur, gas da ɗanyen mai kashi 80 bisa 100 ga Isra’ila, bayan kotu ta yanke hukuncin haramcin cinikin a cikin watan Janairu.
Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira a sa wa waɗannan ƙasashe takunkumi domin hana su ci gaba da wannan haramtaccen ciniki da Isra’ila, a cewar jaridar.
Binciken ya gano cewa kamfanonin da ke sayar wa Isra’ila mai ɗin na haɗin gwiwa ne tsakanin ƙasashen da ake haƙo man da kuma kamfanonin da ke sayar da man ga Isra’ila.
Ya zuwa ranar 15 ga Agusta dai Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta ce Isra’ila ta kashe mutum 40,005, ta raunata 92,401. Sannan kuma mutum sama da miliyan 2.3 sun rasa muhallin su.
