News
Shugabar Kungiyar Matan Jami’an Kwastom Ta Bude Ofishin COWA Reshen PTML
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugabar kungiyar matan jami’an hukumar kwastom, Misis Kikelomo Adeniyi, ta bude sabon ofisbin COWA na PTML dake jihar Legas a ranar Laraba 28 ga watan Agusta na 2024.
Taron bude ofishin da ya gudana a PTML Mile 2, ya samu halartar shugabannin kungiyar COWA da kwanturololin yanki na hukumar kwastom shiyya ta A.
Zargin ɓata Suna :Kotu ta tura ɗan jarida gidan yari saboda ɓata sunan Gwamnatin Abba
Da take jawabi a yayin taron, Misis Adeniyi tayi bayanin cewa taron bude ofishin ya nuna kokarin kungiyar na horaswa da bunkasa mambobinta. “A yau ba muna iya bude ofishi bane, har ma da bada jari ga wadanda suka samu horo da kayayyakin aiki. Wannan tallafi ya nuna kokarin mu na horaswa da karfafawa”
Ta bayyana godiya fa Kwanturola Tenny Daniyan, babban jami’in kwastom na PTML bisa goyan baya da hadin kai da yake baiwa kungiyar ta COWA.
“Shugabancinka da kokarin na ganin an samu walwala ya kasance abu mai kima kuma muna yabawa da dama da tallafin da ka bamu”, inji ta.
Misis Adeniyi ta kuma jaddada kudurin kungiyar na horas da mata domin su dogara da ka su.
” A kungiyar COWA, magana ake ta koya sana’o’i da mayar da matanmu suna dogaro da kansu, suna zuciyarsu ko sun kasance matan jami’an da suka rasu ne ko matan jami’an dake kan aiki ko ma al’umma gabadaya”.
Anata jawabin, shugaban kungiyar COWA reshen PTML, Misis Maureen Daniyan, ta bayyana rawar da kungiyar matan jami’an kwastom ke takawa a matsayin wani ginshiki na tallafi. “A reshen COWA na PTML, mun sanya tsare-tsare don cimma ci gaba. Bude cibiyar koyar da sana’o’i na daya daga cikin kokarin da muke yi. Muna fatan yin kari yayin da Ubangiji yake bamu karfi”.
Wadanda suka samu horo a fannin girki da gyaran jiki da sauran sana’o’i, sun karbi kayayyakin aiki. Haka kuma an rabawa zawara tallafin kayan abinci da kudi.
Haka kuma, an nishadantar da mahalarta taron da wasannin kwaikwayo da mambobin kungiyar suka gabatar kan ayyukan da COWA ke yi.
