Connect with us

News

Rundunar Yan Sanda Ta Kama Wani Matashi Da Laifin Sace Wata Kankanuwar Yarinya ‘Yar Shekara 4 A Kano 

Published

on

Rundunar Yan Sanda Ta Kama Wani Matashi Da Laifin Sace Wata Kankanuwar Yarinya 'Yar Shekara 4 A Kano

DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rundunar ‘Yan-sandan Kano ta ce ta samu nasarar kama wani matashi mai suna Saifullahi Abba dan shekara 23 mazaunin unguwar kofar Fada a garin Wudil da ke jihar ta da zargin  laifin sace wata kankanuwar yarinya ‘yar shekara 4 yayi garkuwa da ita.

Advertisement

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce matashin ya sace kankanuwar yarinyar ce mai suna Nabila.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Tan 1,500 Na Irin Alkama

A cewar sanarwar tun farko mahaifin yarinyar mai suna Zulkiflu Abdullahi mazaunin kauyen Dakatsalle da ke yankin karamar hukumar Bebeji shi ne ya shigar da korafi ofishin ‘yan-sanda ya shaida cewa, an sace ‘yarsa’ ‘yar shekara 4 sannan wadanda suka saceta sun kirashi sun bukaci ya basu kudin fansa Naira miliyan 3.

Advertisement

Abdullahi Haruna Kiyawa ta cikin sanarwar dai ya ce bayan bincike da rundunar ta yi ta samu nasarar kama Saifullahi Abbaa kauyen Luran da ke karamar hukumar Dawakin kudu, inda daga nan ne ya kaisu inda ya boye yarinyar , kuma tuni yansanda sun ceto yarinyar har sun kaita asibiti an duba lafiyarta, kalau take.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending