Connect with us

News

Idan Kana Azumi Kada Ka Rasa Waɗannan Abubuwa 11  – Sheikh Daurawa

Published

on

Daurawa
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta a watan Ramadan.

Advertisement

Yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumi, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa akwai ɗimbin lada ga duk wanda ya aiwatar da waɗannan ayyuka kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito

 

Advertisement

1. Azumi

 

Advertisement

Ya kamata mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncensa, ya kiyaye su, tare da nisantar duk wani abu da zai rage lada ko karya azumi.

 

Advertisement

2. Sallah

 

Advertisement

A dage da yin sallolin farilla a cikin jam’i, tare da Sallar Taraweeh da Tahajjud, domin samun lada mai yawa.

 

Advertisement

3. Ciyarwa

 

Advertisement

Ciyar da mai azumi yana da lada mai girma, ko da dabino ko ruwan sanyi ne. Sheikh Daurawa ya ambato hadisin Annabi (SAW) da ke cewa: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, zai samu lada kamar ya yi azumin.”

 

Advertisement

4. Umrah

 

Advertisement

Ga wanda yake da hali, yin Umrah a watan Ramadan yana da lada mai girma. Idan ba shi da hali, ya maye gurbinsa da ciyar da masu azumi.

 

Advertisement

5. I’tiƙafi

 

Advertisement

Yin I’tiƙafi na daga cikin manyan ibadu, musamman a kwanaki goma na ƙarshe na Ramadan, domin nesantar shagalin duniya da kuma tsayawa domin ibada.

 

Advertisement

6. Daren Lailatul Ƙadar

 

Advertisement

Sheikh Daurawa ya shawarci Musulmi da su dage da neman dacewa da daren Lailatul Ƙadar ta hanyar yin salloli, addu’o’i da sauran ayyukan alheri.

 

Advertisement

7. Yafiya

 

Advertisement

Yafiya na daga cikin halayen da Allah ke so. Sheikh Daurawa ya bukaci Musulmi da su yafe wa juna domin neman gafarar Allah a cikin wannan wata mai alfarma.

 

Advertisement

8. Karatun Al-Ƙur’ani

 

Advertisement

Yawaita karatun Al-Ƙur’ani yana da lada mai yawa, domin a watan Ramadan aka saukar da shi.

 

Advertisement

9. Addu’a

 

Advertisement

Yana da muhimmanci a dage da addu’a, musamman a lokacin Sahur, buɗa-baki da lokacin da ake cikin azumi, domin a waɗannan lokuta Allah na karɓar addu’o’i.

 

Advertisement

10. Zumunci

 

Advertisement

Sada zumunta yana ƙara albarka, arziƙi da zaman lafiya.

 

Advertisement

11. Tausayi

 

Advertisement

Azumi yana koyar da tausayi da taimakon marasa hali, domin mai azumi yana jin halin da masu buƙata ke ciki, hakan zai sa ya ƙara taimako da jin ƙansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending