News
Yanbindiga Sun Kai Hai Wani Gidan Marayu A Kogi
‘Yan bindiga sun kai hari wani gidan marayu a Jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai 23 a wani hari da ke nuna tabarɓarewar matsalar tsaro a ƙasar.
Hukumomi sun tabbatar cewa an ceto yara 15, yayin da takwas ke hannun masu garkuwa da su.
An kai harin ne a wani yanki mai keɓe a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, kamar yadda Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya bayyana.
An ce makarantar da aka kai hari, wato Dahallukitab Group of Schools, tana aiki ba bisa ƙa’ida ba a lokacin farmakin.
Hukumomi sun ce har yanzu ba a gano ko su waye maharan ba, kuma babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin.
Kalmar “ɗalibai” na nuni da cewa yawancin waɗanda abin ya shafa ƙananan yara ne na firamare ko ƙasa da haka.
Hukumomin tsaro, ƙarƙashin jagorancin rundunar ‘yansandan Nijeriya a Jihar Kogi, sun kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun rahoton harin.
Fanwo ya ce haɗin gwiwar jami’an tsaro ya taimaka wajen ceto yara 15 daga cikin waɗanda aka sace.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan domin ceto sauran yara takwas da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.
Satar ɗalibai ta zama wani abin da ke ywan faruwa a Nijeriya, musamman a yankin arewa ta tsakiya da ma arewan gaba ɗaya, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke yawan kai hari makarantu da kan al’ummomi masu rauni domin neman kuɗin fansa.
Nijeriya na ci gaba da fuskantar matsananciyar matsalar tsaro mai rikitarwa, inda ƙungiyoyin ‘yanta’adda da na masu laifi ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar, abin da ke ƙara haddasa rashin kwanciyar hankali da fargaba a tsakanin jama’a.
