Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Kilo 748 Na Tramadol A Hanyar Benin zuwa Legas

Published

on

1777336980678

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Edo ta sanar a ranar Litinin cewa ta kama magungunan, ciki har da tramadol mai nauyin kilo 748.02, a kan babbar hanyar Benin zuwa Legas.

Kwamandan NDLEA na Jihar Edo, Mitchell Ofoyeju, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa yayin da yake gabatar da nasarar aikin rundunar ga manema labarai a Benin.

Advertisement

Siyasa Ce Ta Fi Dacewa Da Malamai Ba Kamasho Ba —Malam Ibrahim Khalil

Ya ce: “A ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026, ƙoƙarin rundunar na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ya kai ga kama wata babbar mota kirar Mercedes-Benz mai ɗauke da tambarin Kungiyar ‘Yan Kwadago ta Kasa (NLC) mai lambar NLC 146 FC.

Advertisement

“An gano cewa motar na ɗauke da kwalaye 95 masu ɗauke da kapsul da ƙwayoyi har miliyan 1.196 na magungunan da ake amfani da su ga masu taɓin hankali a Asibitin kula da lafiyar kwakwalwa, waɗanda aka ɗauko su daga Legas zuwa Onitsha a Jihar Anambra.

“An kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi mambobin ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi ne, Osagie Igbinibo mai shekaru 43 da Omijie Malik mai shekaru 44, dangane da wannan kamen.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending