News
CBN Ya Soke Lasisin Bankunan Microfinance 46

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin aiki na ƙananan bankuna na microfinance 46 a fadin ƙasar, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2026.
A cikin wata sanarwa da CBN ya fitar, an bayyana cewa an dauki matakin ne bisa ikon da aka ba bankin a karkashin Sassan 12 da 13 na Dokar Bankuna da Sauran Hukumomin Kuɗi (BOFIA) ta shekarar 2020.
Shugaban FCAPT Kano Ya Yabawa Gwamnatin Kano Kan Gudanar da Rijistar Katin Zaɓe A Makarantar
CBN ya ce an amince da soke lasisin ne daga Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso, bayan bankunan sun kasa cika muhimman ka’idojin da ake bukata domin ci gaba da gudanar da aiki a matsayin cibiyoyin kuɗi da aka bai wa izini.
Babban Bankin ya bayyana cewa dalilan da suka haifar da wannan mataki sun haɗa da ƙarancin kadarori da ba sa iya biyan basussuka, rufe aiki ba tare da amincewar CBN ba, da kuma dakatar da harkokin kuɗi gaba ɗaya.
Sauran dalilai sun haɗa da rashin fara aiki cikin watanni 12 bayan samun lasisi, da kuma gaza kiyaye mafi ƙarancin jarin da ba ya lalacewa saboda asara.
CBN ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na kare kwanciyar hankali a fannin kuɗi, kare masu ajiya, da tabbatar da bin ka’idoji daga duk cibiyoyin kuɗi da ke aiki a ƙasar.
Haka kuma bankin ya jaddada cewa zai ci gaba da ɗaukar matakan sa ido da doka domin tabbatar da ingantaccen tsarin kuɗi mai aminci da ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin banki a Nijeriya.
A jerin bankunan da abin ya shafa akwai Microfinance Bank daban-daban daga jihohi da birane ciki har da Lagos, Kano, Abuja, Abia, Ogun, Kaduna da sauransu, wadanda suka haɗa da Gold MFB, Creditville MFB, CASHA MFB, Supreme MFB, da Avanus MFB.
CBN ya ƙara da cewa wannan mataki zai taimaka wajen tsaftace tsarin microfinance a Nijeriya tare da ƙarfafa bankunan da ke aiki bisa ƙa’ida da ƙarfi.
