Connect with us

News

Sojoji 104 Sun Tsere Daga Bakin Aikinsu

Published

on

82471 e1759247106578
Advertisements
ads

Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta bayyana cewa kimanin sojoji 104 ne aka nema aka rasa daga bataliya ta 162 da ke kan hanyar Mandara zuwa Buratai a jihar Borno. Rundunar ta bayyana cewa sojojin sun gudu ne daga fagen daga tare da bindigunsu bayan wani gagarumin hari da aka kai matsuguninsu.

Idan za a iya tunawa ranar 5 ga watan Yunin 2026 wasu ƴan ta’adda da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar ISWAP ne sun kai hari zuwa sansanin sojojin da daddare, a daidai lokacin da ake sheƙa ruwan sama.

CBN Ya Soke Lasisin Bankunan Microfinance 46 

Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa bayanan da su ke hannunta na ranar 5/06/2026, ana zargin sojojin sun tsere ne tare da makamansu a lokacin da su ke fagen daga yayin harin ƴan ta’addar a ranar.

Cikin wata sanarwa ta bakin Lutanal FI Ndubuisi ya bayyana cewa, wani soja mai suna Idris Mohammed tare da ƴan uwansa su 103 sun gudu daga inda aka tura su zuwa wani wurin da ba a sani ba tare da makansu, bayan hari daga ƙungiyar ta’addar Boko Haram ko ISWAP a sansaninsu.

Ya ƙara da cewa a dalilin haka yana tabbatar da cewa har zuwa yanzu ba su dawo bakin aiki ba, saboda haka an bayyana su a matsayin waɗanda su ka tsere daga fagen daga.

Advertisement

Rundunar sojin ta bayyanawa Sahara Reporters cewa an sanar da kowanne sashe na sojojin a faɗin ƙasar nan, cewar su kama tare da miƙa waɗanda abin ya shafa duk inda su ka gansu. Ya ƙara da cewa tuni aka rufe asusun ajiyar bankunan sojojin su 104.

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoton, rundunar sojin Najeriya ba ta saki wata sanarwa a hukumance dangane da batun ba, sakamakon mai magana da yawun rundunar, Kanal Appolonina Anele, ba ta amsa saƙon kiraye-kirayen wayar da aƙonni da aka tura mata dangane da batun ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending