Connect with us

Uncategorized

An samar da shafin Facebook mai suna “Tsaro da Shari’a” domin kawo sahihan labaran Tsaro da Shari’a.

Published

on

IMG 20260707 WA0010

An ƙaddamar da wani sabon shafin Facebook mai suna TSARO da SHARI’A  wanda aka keɓance domin yaɗa sahihan labaran da suka shafi harkokin tsaro da shari’a da kuma ayyukan hukumomin tsaro a Najeriya.

Shafin ya samu karɓuwa ne sakamakon haɗin gwiwar wasu gogaggun ‘yan jarida daga Arewacin Najeriya, waɗanda suka haɗa ƙwarewarsu domin samar wa al’umma sahihan bayanan Tsaro da shari’a da kuma yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya.

ICPC Ta Kama Likitan El-rufai Bayan Ganawa Da Shi ‎

Shafin zai dinga samar da ingantattun labarai daga hukumomin tsaro da kotuna da sauran hukumomin da abin ya shafa, tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin bin doka da oda da kuma rawar da kowa zai taka wajen tabbatar da zaman lafiya.

Sun kuma yi kira ga al’umma da su bi shafin na “Tsaro da Shari’a” a Facebook, domin samun sahihan labarai da bayanai kan lokaci, tare da tallafa wa ƙoƙarin yaƙi da yaɗuwar labaran da ba su da tushe.

A karshe mawallafan shafin sun tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki bisa ƙa’idodin aikin jarida da gaskiya da adalci da tabbatar da sahihancin labari kafin wallafawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending