Uncategorized
Kaduna: Ma’auratan Da Aka Sace Tare Da Jaririyarsu Sun Kuɓuta
Ma’auratan da aka yi garkuwa da su tare da jaririyarsu mai watanni shida a Millennium City, da ke Jihar Kaduna, sun kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Ahmed Abubakar Zakka, matarsa Fatima da jaririyarsu sun kuɓuta ne a ranar Alhamis.
Rahoton ya ce a lokacin da ake haɗa labarin, iyalan suna kan hanyarsu ta komawa cikin birnin Kaduna.
Wani jami’in tsaro mai ritaya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa wakilin jaridar da sakin mutanen.
Ya ce ƙoƙarin da tawagarsa, tare da wasu mutane masu zaman kansu, suka yi ne ya taimaka wajen kuɓutar da iyalan.
An yi garkuwa da Zakka, matarsa da jaririyarsu daga gidansu da ke Millennium City, a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, a ranar 6 ga Oktoba, 2026.
Kwanaki bayan sace su, wani bidiyo da ke nuna Zakka da jaririyarsa a hannun masu garkuwa da mutane ya bazu a kafafen sada zumunta.
Lamarin ya jawo fushin jama’a a faɗin Najeriya, inda mutane da dama suka nuna damuwarsu kan sace iyalan, musamman kasancewar jaririyar ba ta wuce watanni shida da haihuwa ba.
