Connect with us

Kasuwanci

PAN Ta Bukaci Gwamnatoci Su Bai Wa Noma Da Kiwo Muhimmanci Kamar Tsaro

Published

on

IMG 20261118 132130 491
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Shugaban Ƙungiyar Masu Kiwon Kaji ta Nijeriya (PAN), reshen Jihar Kano, Dr Usman Gwarzo, ya buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai da su bai wa harkokin noma da kiwo muhimmanci kamar yadda suke bai wa harkokin tsaro kulawa.

Dr Usman Gwarzo ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin taron masu kiwon kaji na  Arewacin Nijeriya na shekarar 2026 (Northern Nigeria Poultry Conference and Exhibition), wanda aka gudanar a Kano ranar Laraba.

An Daure Sama Da Mutum 200 Kan Hakar Zinare Ba Bisa Ka’ida Ba

Ya ce bai wa noma da kiwo muhimmanci zai taimaka wajen magance ƙalubalen da ke addabar waɗannan fannoni, tare da bunƙasa samar da abinci da tattalin arzikin ƙasa.

Taron ya samu halartar masana harkar noma da kiwo daga sassa daban-daban na Nijeriya, da kuma wakilan Ƙungiyar Manoman Kaji daga jihohi da dama, ciki har da Kaduna, Gombe, Katsina da Yobe.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo ta Jihar Kano, Dr Aliyu Isah Aliyu, ya bayyana aniyar gwamnatin jihar ta haɗa hannu da ƙungiyar wajen samar da kayayyakin tallafi ga masu kiwon kaji a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Advertisement

Kwamishinan ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙarfafa sana’ar kiwon kaji da inganta harkokin kasuwanci ga masu gudanar da ita.

Ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau da zai sauƙaƙa harkar kiwon kaji da bunƙasa ta a faɗin jihar.

An gudanar da taron ne domin tattauna hanyoyin magance ƙalubalen da ke fuskantar masana’antar kiwon kaji, da kuma duba damarmakin zuba jari, ƙirƙire-ƙirƙire, bunƙasa kasuwanci da samar da haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.

Ana sa ran tattaunawar za ta taimaka wajen bunƙasa masana’antar kiwon kaji a Arewacin Nijeriya da ƙarfafa gudummawar da take bayarwa wajen samar da abinci da ayyukan yi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending