Labarai
Jami’an Tsaro Su Guji Yin Barazana Ga Yan Jaridu Yayin Gudanar da aikinsu —

Ministan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Najeriya, Mohammed Idris, ya bukaci jami’an tsaro da su rika mutunta hakkokin ‘yanjarida tare da tabbatar da tsaronsu yayin gudanar da ayyukansu.
Ministan ya bayyana hakan ne a taron koli kan tsaro da aikin jarida a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, wanda aka gudanar a Coronation Hall, da ke gidan gwamnatin Kano.
INEC Za Ta Gwada Na’urar BVAS A Rumfunan Zabe 17,656 Ranar 28 Ga Nuwamba
Taron mai taken “Aikin Jarida a Yanayin Kalubalen Tsaro: Kariya, Kwarewa da Hadin Kai tsakanin ‘Yanjarida da Jami’an Tsaro” ya samu halartar jami’an tsaro, ‘yanjarida da sauran masu ruwa da tsaki.
Ministan, wanda Malam Jibrin Baba Ndace ya wakilta, ya ce wajibi ne jami’an tsaro su fahimci muhimmancin aikin ‘yanjarida da hakkokinsu na tattara bayanai da yada labarai ga al’umma.
Ya kuma bukaci kafafen yada labarai su rika horas da ma’aikatansu kan ka’idojin aikin jarida, musamman wadanda ke aiki a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
Mohammed Idris ya jaddada cewa ‘yanjarida ma suna da alhakin kare kansu yayin gudanar da ayyukansu, tare da kauce wa yada labaran karya da za su iya haddasa rudani ko tashin hankali a cikin al’umma.
Kungiyar ‘Yanjarida ta Najeriya (NUJ), karkashin jagorancin Shugabanta na Kasa, Kwamared Alhassan Yahaya, ce ta shirya taron.
Daga cikin manyan baki da suka halarta akwai Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Mataimakinsa Murtala Sule Garo ya wakilta, Farfesa Ali Pate, Farfesa Sule Ya’u Sule, tsohon Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Janar Sani Kuka Sheka, da sauran masu ruwa da tsaki.
