Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarrayya Za Ta Bai Wa Teloli 600 Tallafin Naira Miliyan 5 Kowannensu

Published

on

sallah
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shirin tallafa wa masu sana’ar ɗinki guda 600 a faɗin Najeriya, inda za a bai wa kowane mutum tallafin kuɗi da na bunƙasa sana’a har Naira miliyan biyar.

An bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Ba Zan Taba Yin Sulhu Da Yan Ta’adda Ba —Gwamnan Jihar Zamfara

Daraktar sashen shari’a ta ITF, Safiya Abubakar, wadda ta yi magana a madadin Darakta Janar na hukumar, Afiz Oluwatoyin Ogun, ta ce shirin zai ɗauki tsawon shekaru biyar domin taimaka wa waɗanda aka zaɓa su bunƙasa sana’o’insu, su samu ƙarfin gudanar da kasuwanci mai ɗorewa tare da samar da guraben ayyukan yi ga sauran ’yan Najeriya.

Shirin, wanda Asusun Horar da Ma’aikata (ITF) ke jagoranta, zai ci Naira biliyan uku cikin shekaru biyar domin taimaka wa teloli su kafa sana’o’insu, ƙarfafa su da kuma faɗaɗa ayyukansu.

A matakin farko na shirin, an zaɓi masu sana’ar ɗinki guda 150 daga yankin Arewa ta Tsakiya, waɗanda za su fara cin gajiyar tallafin.

Advertisement

Wannan matakin farko na shirin zai lakume kimanin Naira miliyan 750.

Hukumar ta bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na shirin Skill-Up Artisans Programme, kuma a buɗe yake ga waɗanda suka halarci horon da kuma waɗanda ba su halarta ba, matuƙar sun ci jarrabawar tantance ƙwarewar ITF tare da samun lasisin da ake batata.

A cewar hukumar, manufar shirin ita ce rage matsalolin rashin jari da kayan aiki na zamani da masu sana’ar ke fuskanta, tare da taimaka musu su sauya ƙwarewar ɗinki zuwa kasuwanci mai ɗorewa.

 

 

PUNCH

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending