News
Buhari ya sa hannu kan kasafin 2022 na naira tiriliyan 17.127
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2022 inda ya zama doka.
Kasafin ya kai naira tiriliyan 17.127 wanda aka yi wa laƙabi da kasafin habaƙa tattalin arziƙi da tafiyar da shi.
Cikin waɗanda suka halarci sa hannu a kasafin kuɗin har da Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan da Kakakin Majalsar Wakilai Femi Gbajabiamila da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Ministar Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare Zainab Ahmed.
Shekarar 2021 mai ƙarewa an yi mata kasafin naira tiriliyan 13.588 inda daga baya aka ƙara biliyan 983 a kai.