Connect with us

News

Sama Da Dalibai Miliyan Biyu Ne Za Su Rubuta Jarabawar JAMB Ta Bana

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta ƙasa (JAMB) ta bayyana cikakken shirinta na gudanar da jarabawar UTME ta shekarar 2026, inda ta ce sama da dalibai miliyan 2.2 ne ake sa ran za su rubuta jarabawar a fadin Najeriya.

A cewar hukumar, za a fara gudanar da jarabawar ne daga ranar 16 zuwa 22 ga watan Afrilu, 2026, a cibiyoyi 966 da aka tantance na gwajin kwamfuta (CBT) a fadin ƙasar.

Advertisement

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ɗalibai A Hanyar Zuwa Jarrabawar JAMB

JAMB ta ce ta kammala shirye-shiryenta bayan tantance cibiyoyin jarabawar, inda ta cire cibiyoyi 23 da ba su cika ka’idojin da ake bukata ba a lokacin gwajin gwaji (Mock-UTME) da aka gudanar kwanan nan.

Advertisement

 

Hukumar ta umarci dalibai da su buga takardun sanarwar jarabawarsu ta hanyar shafin intanet na hukuma, domin samun muhimman bayanai kamar ranar jarabawa, lokaci, wurin rubuta jarabawa da kuma umarnin da suka shafi tantance sahihanci (biometric verification).

Advertisement

 

Haka kuma, ta shawarci dalibai da su san cibiyoyin da aka ware musu kafin ranar jarabawa domin kauce wa jinkiri ko wata matsala a ranar rubuta jarabawar.

Advertisement

 

Dangane da masu bukata ta musamman, JAMB ta ce ta tanadi tsare-tsare na musamman domin dalibai masu nakasa karkashin shirin JAMB Equal Opportunity Group (JEOG).

Advertisement

 

A bangaren tsaro da sahihancin jarabawa, hukumar ta gargadi dalibai da su guji duk wata magudi, tana mai jaddada cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa dokokin da suka tanada.

Advertisement

 

Haka kuma, ta ce an kara tsaurara matakan tsaro da kuma amfani da sabbin fasahohi domin gano da hana magudi a duk cibiyoyin jarabawar.

Advertisement

 

Shugaban hukumar, Farfesa Is’haq Oloyede, ya bukaci jami’an da ke kula da jarabawar da su nuna kwarewa da da’a, yana mai cewa nasarar jarabawar na dogara da yadda suke gudanar da aikinsu.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa an cire jami’ai 11 daga aikin saboda rashin kwarewa, yana mai cewa za a dauki karin matakan ladabtarwa idan bincike ya tabbatar da hakan.

A karshe, JAMB ta jaddada kudirinta na gudanar da jarabawa mai inganci, gaskiya da adalci, daidai da ka’idojin kasa da kasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending