Sports
Akwai Jan Aiki A Gaba – Kocin Manchester United Rangnick
Daga Hamza Yusuf Yobe
Mai horar da ‘yan wasan Manchseter United Ralf Rangnick, ya ce akwai jan aiki a gaba muddin kungiyar na so ta yi zarra a nan gaba.
Ranganick ya bayana hakan ne bayan kayen da United ta sha hannun Wolverhampton da ci daya mai ban haushi.
Wannan shi ne kaye na farko da kungiyar ta fuskanta karkashin sabon kocin dan asalin kasar Jamus.
A karshen watan Nuwamba aka nada Rangnick a matsayin kocin wucin gadi bayan da aka sallami Ole Gunner Solskjaer.
“Ko kadan ba mu taka rawar a zo a gani ba, wannan wasa ya nuna cewa muna da aiki babba a gabanmu da za mu yi.” Ranganick ya ce kamar yadda AP ya ruwaito.
A minti na 82 dan wasan Wolverhampton Joao Moutinho ya zura kwallo a ragar United a wasan da suka kara a gasar Premier League.