Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Rudiger, Botman, Trippier, Christensen, Barbosa, Maitland-Niles

Published

on

Spread the love

Daga Hamza Yusuf Yobe

Real Madrid da Paris St-Germain da Bayern Munich da kuma Juventus duka sun fara tattaunawa da wakilan Antonio Rudiger kan yarjejeniyar sayen dan bayan na Chelsea da Jamus wanda kwantiraginsa zai kare a bazara. (Sky Sports)

Lille ta gaya wa Newcastle cewa dan bayanta na Holland Sven Botman, ba na sayarwa ba ne bayan da kungiyoyin suka tattauna a kan farashin kusan fam miliyan 30. (Telegraph – subscription required)

Advertisement

Amma kuma Newcastle din ta kusan cimma nasara a tattaunawar sayen dan bayan Atelitico Madrid dan Ingila Kieran Trippier, inda ciniki yake dab da fadawa a kan kusan fam miliyan 25. (Express)

Tattaunawar kara tsawon kwantiragin dan wasan Chelsea Andreas Christensen ta kara cijewa, inda Barcelona take da sha’awar sayen dan bayan na Denmark a watan Janairu, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara. (Gianluca Di Marzio – in Italian)

West Ham ta tattauna kan sayen dan gaban Brazil Gabriel Barbosa, daga kungiyar Flamengo. (Sky Sports)

Advertisement

Roma ta mika bukatar karbar aron dan wasan tsakiya na Ingila Ainsley Maitland-Niles, daga Arsenal har zuwa karshen kakar nan, da yuwuwar saye shi a bazara. (Athletic – subscription required)

Za a gwada lafiyar dan bayan Scotland Nathan Patterson, a Everton bayan da kungiyarsa Rangers ta nuna alamun yarda da tayin farko na fam miliyan 12, wanda zai iya karuwa zuwa fam miliyan 16 da karin wasu ‘yan tsarabe-tsarabe. (Football Insider)

AC Milan na tattaunawa domin sayen dan wasan tsakiya na Portugal Renato Sanches, daga Lille. (Calciomercato – in Italian)

Advertisement

Dan wasan gaba na Uruguay Luis Suarez, yana son barin Atletico Madrid idan kwantirginsa ya kare a bazara, saboda yana son sake hadewa da Lionel Messi a kungiyar Inter Miami ta Amurka. (El Nacional – in Catalan)

Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce kungiyar ta dawo a matsayin gagara-badau, da yake magana a kan yuwuwar sayen dan wasan Norway Erling Braut Haaland, daga Borussia Dortmund. (Mirror)

Maganar tafiyar Alvaro Morata Barcelona kusan ba za ta yuwu ba da kashi kusan 95 cikin dari saboda tuni kungiyar dan wasan na Sifaniya Atletico Madrid ta riga ta cimma yarjejeniya da Juventus inda yake zaman aro. (AS – in Spanish)

Advertisement

Barcelona ba ta da wani shiri na tattaunawa da Ousmane Dembele, duk da cewa dan wasan na Faransa wanda kwantiraginsa zai kare a bazara bai yanke shawara ko zai ci gaba da zama a Barcan ba. (AS – in Spanish)

Bournemouth ta cimma yarjejeniyar sayen dan bayan Manchester United Ethan Laird, wanda ya kwashe rabin lokacin wannan kaka a matsayin aro a Swansea City. (Football Insider)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *