Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Rudiger, Ronaldo, Tielemans, Luiz, Vestergaard, Dest, Spence, Garner
Barcelona ta yi yunkurin cin moriyar takunkumin da aka sanya wa Chelsea, inda za ta dauke mata ‘yan bayanta guda uku, Antonio Rudiger, da Cesar Azpilicueta, da Andreas Christensen. (Telegraph – subscription required)
Manchester United na sa ran Cristiano Ronaldo, mai shekara 37,ya bar kungiyar a karshen kakar da ake ciki, saura shekara daya ke nan ya kammala kwantiraginsa na shekara biyu. (Football Insider)
Leicester City na fatan shawo kan dan wasanta na tsakiya dan Belgium Youri Tielemans, mai shekara 24, ya sanya hannu a sabon kwantiragi, duk da sha’awarsa da Manchester United da Arsenal ke yi. (Team Talk)
Dan wasan tsakiya na Aston Villa Douglas Luiz, mai shekara 23, dan Brazil ka iya barin kungiyar a bazaran nan saboda kociyansu Steven Gerrard, ya tsara sayen wani babban dan wasan tsakiya a jeri na farko cikin ‘yan wasan da zai nema a kaka mai zuwa. (Mail)
Everton na shirin sayen dan bayan Leicester City dan Denmark Jannik Vestergaard, mai shekara 29 a bazaran nan. (Football Insider)
Leeds United na duba yiwuwar sayen dan bayan Barcelona da Amurka Sergino Dest, mai shekara 21. (Team Talk)
Dan bayan Middlesbrough Djed Spence, wanda ke zaman aro a Nottingham Forest, yana son tafiya wata kungiyar Premier yayin da Arsenal da Tottenham suke shirin taya shi fam miliyan 20 a bazara, sannan kuma Manchester United ma na sha’awar dan tawagar Ingilar ta ‘yan kasa da shekara 21. (Mirror)
Nottingham Forest na son saye dan wasan Ingila na tsakiya James Garner wanda ta aro daga Manchester United domin ya yi zaman dindindin, sai dai hakan ya dogara ne ga samun nasarar kungiyar tsallakawa zuwa gasar Premier. (Football Transfers)
ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
RB Leipzig za ta tattauna batun kwantiragi da dan wasanta na takiya Christopher Nkunku, mai shekara 24, a bazaran nan, amma kuma za ta saurari tayin da ya zarta yuro miliyan 75 a kan dan wasan na Faransa ba. Manchester United da Liverpool da Paris St-Germain da Real Madrid da Manchester City da Arsenal da Bayern Munich na sa ido a kan lamarin dan wasan. (ESPN)
Tottenham ta gabatar da tayin fam miliyan biyu a kan dan bayan Oxford United Luke McNally, dan Ireland mai shekara 22. (Football Insider)
Liverpool na shirin sayen matashin dan gaba na gefe na tawagar Scotland Ben Doak mai shekara 16 daga Celtic a kan fam dubu 600. (Goal)
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
