Connect with us

Sports

Gwamnati ta fara bincike kan ragargaza filin wasa na Abuja da ‘yan kallo suka yi

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta rantsar da wani kwamati da zai bincika abin da ya faru bayan tashi daga wasa tsakanin Najeriya da Ghana, inda wasu ‘yan Najeriya suka kutsa tsakiyar fili tare da kai hare-hare kan mutane.

Advertisements
Advertisements

Jim kaɗan bayan hura usur ɗin ƙarshe a yammacin Talata da ta gabata, dubban ‘yan kallo suka afka wa filin wasan na Moshood Abiola National Stadium ƙunshe da fushin doke su da tawagar Black Stars ta yi a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2022.

Advertisements

Wasu bidiyo da aka dinga yaɗawa a shafukan zumunta sun nuna magoya baya na lalata wasu kayayyaki na filin wasan da kuma yin watsi da kayan wasanni.

Advertisements
Advertisements

‘Yan Najeriya da dama sun yi Allah-wadai da wannan ɗabi’ar, suna masu cewa “wasa ba hauka ba ne”.

Social embed from twitter

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending