Sports
Spanish Super Cup: An tsayar da ranar wasan Real Madrid da Barcelona Sa’o’i 5 da suka wuce
Daga Yasir Abdullah
Za a buga wasan daf da karshe a Spanish Super Cup tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar 12 ga watan Janairun 2022.
Daya karawar za a yi ne tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao ranar 23 ga watan Janairun 2022.
Za a buga wasannin a filin wasa na King Fahd da ke Riyadh a Saudi Arabia.
Ana buga Spanish Super Cup ne tsakanin kungiyoyi hudun da suka yi fice a wasannin gasar Spaniya da ta gabata.
Atletico Madrid ce ta lashe kofin La Liga na bara, inda Real Madrid ta yi ta biyu a babbar gasar ta Sifaniya.
Barcelona ce ta lashe Copa del Rey a kakar da ta gabata, sannan Athletic Bilbao ta yi ta biyu.
Za a buga wasan karshe a Spanish Super Cup na bana ranar Lahadi 16 ga watan Janairu a dai filin na King Fahad da ke Saudi Arabia.
An fara Spanish Super Cup a 1982, kuma Real Sociedad ce ta lashe kofin, bayan da ta yi rashin nasara a wasan farko da ci 1-0 a hannun Real Madrid ranar 13 ga watan Oktoban 1982.
A wasa na biyu ta doke Real Madrid da ci 4-0 ranar Talata 28 ga watan Disambar 1982.