Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Aubameyang, Haaland, Vlahovic, Kessie, Nketiah, Dembele
Daga Yasir sani Abdullah
Arsenal za ta saurari tayin da duk wata kungiya za ta yi wa Pierre-Emerick Aubameyang, wanda zai iya barin kungiyar a wannan watan na Janairu.
Gunners din ta gabatar da tayin yuro miliyan 70 ga Fiorentina a kan dan wasan gaban Serbia Dusan Vlahovic, abin da zai sa tafiyar dan wasan tsakiya na Uruguay Lucas Torreira kungiyar ta Serie A ta zama ta dindindin.
Dan wasan gaba na Red Bull Salzburg dan Jamus Karim Adeyemi, shi ne wanda Borussia Dortmund take nema domin maye gurbin Erling Braut Haaland.
Haka kuma dan wasan Fiorentina Vlahovic, da na Stuttgart Sasa Kalajdzic da kuma na Benfica dan Uruguay Darwin Nunez na daga cikin wadanda kungiyar ta Bundesliga ke neman saye.
Borussia Dortmund ta zaku ta ga an kammala batun cinikin Haaland kafin karshen kasuwar ‘yan wasa ta Janairu.
Dan wasan gaba na kungiyar Flamengo ta Brazil Gabriel Barbosa, zai iya tafiya Newcastle United, duk da cewa kungiyar na cikin hadarin faduwa daga gasar Premier.
Dan wasaan tsakiya na Holland Donny van de Beek, zai duba damar da yake da ita a watan nan na Janairu yayin da yake tunanin barin Manchester United.
Kocin Tottenham Antonio Conte zai gana da shugaban kungiyar Daniel Levy domin tattauna batun ‘yan wasan da za su saya a watan nan.
Dan wasan AC Milan na Ivory Coast Franck Kessie, da daga cikin wadanda dan Italiyar yake son saye.
Kungiyoyin Premier Brighton da Crystal Palace na matukar son sayen Eddie Nketiah na Arsenal a watan nan na Janairu.
Blackburn Rovers na son sama da fam miliyan 30 a kan dan wasanta na Chile Ben Brereton Diaz.
Roma na son kammala batun daukar aron Ainsley Maitland-Niles na Arsenal a makon nan.
Paris St-Germain na sha’awar sayen Ousmane Dembele daga Barcelona.