News
Maciji Ya Shiga Wandon Bature
Wani ɗan yawon buɗe ido ɗan ƙasar Jamus mai shekaru 57 ya rasu bayan da maciji ya cije shi a yayin da yake kallon wasan masu sarrafa macizai a wani otel da ke birnin Hurghada na ƙasar Masar.
A cewar jami’an ‘yan sandan Jamus, lamarin ya faru ne a farkon watan nan, lokacin da mutumin ke hutu tare da iyalansa a bakin Tekun Bahar Maliya.
Rahotanni sun ce wasan, wanda ke cikin shirye-shiryen nishaɗin otel ɗin, ya ƙunshi macizai guda biyu da ake zargin nau’in cobra ne, inda mai wasan ke rataye su a wuyan masu kallo domin burge su.
Sai dai hatsarin ya auku ne lokacin da ɗaya daga cikin macizan ya kutsa cikin wandon mutumin, inda ya cije shi a ƙafarsa.
Jami’an tsaro sun ce mutumin ya nuna alamun guba mai tsanani bayan cizon, inda aka yi masa taimakon gaggawa kafin a kai shi asibiti.
Sai dai daga bisani ya rasu duk da ƙoƙarin ceton rayuwarsa.
Hukumomi a Jamus sun ce sun fara gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru, yayin da ake jiran sakamakon gwaje-gwajen sinadaran guba domin gano cikakken bayani kan mutuwar.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, dubban mutane na rasa rayukansu a kowace shekara sakamakon cizon maciji a faɗin duniya.
-
News6 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
