Connect with us

News

Gobara Ta Kone Filaza A Kano 

Published

on

‎Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Talata ta yi barna a wani gini mai hawa biyu da ke Titin Airport, a Ƙaramar Hukumar Fagge dake Jihar Kano, inda ta kone wasu shagunan kasuwanci da ke cikin Filazar.

‎Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar, inda ya ce rundunar gaggawa ta samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 4:01 na asubahin ranar 29 ga Afrilu, 2026.

Advertisement

‎A cewar sanarwar, nan take jami’an kashe gobara daga hedikwata da sauran tashoshin da ke cikin birnin Kano suka garzaya wurin domin dakile yaduwar gobarar.

‎Lokacin da suka isa wurin, sun tarar da ginin — wanda aka mayar da shi filazar kasuwanci mai fadin kusan ƙafa 100 bisa 100 — yana ci da wuta sosai.

Advertisement

‎Bayanan farko sun nuna cewa gobarar ta fi shafar shaguna biyu da ke ƙasa (ground floor) na ginin, musamman waɗanda ke sayar da kayan asibiti.

‎Hukumar ta ce ta tura motoci biyar na kashe gobara daga wurare daban-daban, ciki har da tashoshin Kasuwar Abubakar Rimi, Kantin Kwari, Bompai domin shawo kan lamarin.

Advertisement

‎Sai dai har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike.‎

‎Rahotanni sun ce har yanzu ba a tabbatar da ko an samu asarar rayuka ba a yayin wannan iftila’in.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending