News
Mazauna Ƙauyuka 30 Sun Fice Daga Muhallansu Saboda Rashin Tsaro A Zamfara
mazauna ƙauyuka sama da 30 da ke yankin Mada a Jihar Zamfara, sun tsere daga muhallansu sakamakon fargabar hare-haren ’yan bindiga da ke ƙaruwa a yankin.
Rahotanni daga yankin sun ce mutanen ƙauyukan da ke kewaye da Mada sun fara barin gidajensu ne bayan da suka fuskanci sabbin barazanar hare-hare, lamarin da ya tilasta musu neman mafaka a wurare masu aminci.
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Hutu
Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida cewa janyewar sojojin da aka tura a garin Lilo, bayan sun shafe shekaru suna aikin tsaro, na daga cikin abubuwan da suka ƙara dagula al’amura.
Ya ce, tun bayan janyewar jami’an tsaron, ’yan bindiga suka fara sake samun damar shiga ƙauyukan cikin sauƙi, abin da ya haddasa ƙarin fargaba da kuma tilasta wa jama’a barin muhallansu.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da suka fi fama da matsalar tsaro, inda hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da haddasa asarar rayuka da kuma tilasta wa dubban mutane yin gudun hijira.
Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa kai tsaye kan lamarin ba a lokacin haɗa wannan rahoto, sai dai ana ci gaba da kira ga gwamnati da ta ƙara ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile matsalar tsaron a yankin.
