News
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Juma’a A Matsayin Ranar Hutu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a mai zuwa a matsayin ranar hutu ga ma’aikata a fadin ƙasar, domin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya.
Sanarwar ta fito ne daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ta bakin Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, a yau Laraba a Abuja.
A cewar sanarwar, an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ma’aikata damar yin bikin ranar da ake warewa domin girmama rawar da suke takawa wajen gina tattalin arziki da ci gaban ƙasa.
Ministan ya yabawa ma’aikatan Najeriya bisa jajircewa da ƙwazon aiki, yana mai jaddada cewa gudummawar su na da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa da wadata ƙasa.
Haka kuma, ya bukaci su da su ci gaba da nuna kwarewa da sadaukar da kai a ayyukansu domin ci gaban Najeriya baki ɗaya.
-
News6 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
