Connect with us

News

Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Botman, Dembele, Lewandowski, Timber, Messi, Pogba, Dennis

Published

on

Daga mujahid danlami garba

 

Manchester United ta rubanya kokarinta kan saye ɗan wasan baya a Lille Sven Botman inda suke burin doke AC Milan wajen daidaitawa da ɗan wasan mai shekara 22. (Football Insider)

Advertisement

Ɗan wasan Ajax Jurrien Timber na cikin ‘yan wasan da Manchester United ke hari, ana tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu kan ɗan asalin Netherlands mai shekara 20. (Mirror)

Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce kungiyar ta gabatar wa ɗan wasan gaba a Faransa Ousmane Dembele sabon kwantiragi, sai dai akwai rahotanni da ke cewa ɗan wasan mai shekara 25 ya kwadaitu da wasu kungiyoyin na daban.(Catalunya Radio, via 90 Min)

Advertisement

Barcelona ta tsara kashe euro miliyan 35 wajen saye ɗan wasan Poland Robert Lewandowski, mai shekara 33 daga Bayern Munichhaka zalika tana iya gabatar da irin wannan tayi kan dan wasan Dutch mai shekara 28, Memphis Depay. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Ɗan wasan gaba a Argentina Lionel Messi, mai shekara 34, zai koma Inter Miami a shekara ta 2023 idan kwantiraginsa na shekara biyu ya kare da Paris St-Germain(Direct TV, via Marca)

Advertisement

Sai dai tawagar Messi na musanta cewa zai je Inter Miamisuna cewa bai yanke shawara kan makomarsa nan gaba ba idan ya yi bankwana da PSG(Diario Sport, via Mirror)

Juventus ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Faransa mai buga tsakiya Paul Pogba, wanda kwantiraginsa Manchester United ke karewa a wannan kaka, za a cimma yarjejeniyar shekara uku kan £6.3m ga ɗan wasan. (Goal)

Advertisement

Matthijs de Ligt na Netherlands, mai shekara 22, na gab da cimma yarjejeniyar zama har shekara ta 2026 daJuventus. (Sky Sport Italia, via 90 Min)

Advertisement

Angel di Maria na Argentina mai shekara 34, ya amince da kwantiragin shekara guda a Juventus idan yarjejeniyarsa da Paris St-Germain ta kare a wannan kakar. (Goal)

West Ham na zawarcin ɗan wasan Najeriya mai shekara 24 Emmanuel Dennis daga Watford(Mirror)

Advertisement

Kocin Roma Jose Mourinho na son ya kawo ɗan wasan Serbia mai shekara 33 Nemanja Matic kungiyar. A wannan kakar kwangilar da ya cimma da Manchester United ke karewa. (Calciomercato – in Italian)

Ɗan wasan Ingila James Tarkowski zai yi bankwana da Burnley idan kwantiraginsa ta kare a wannan kakar kuma da alama Newcastle United na son saye ɗan wasan mai shekara 29 (90 Min)

Advertisement

Arsenal, da ake alakantawa da kokarin saye ɗan wasan Manchester City mai shekara 24 Gabriel Jesus, za su fi bada fifiko kan manyan ‘yan wasan da ke kai hari ko da kuwa sun gagara kai wa Champions League. (Telegraph – subscription required)

Barcelona ta hakura ɗan wasanta na baya Samuel Umtiti ya bar kungiyar a wannan kakar, kuma suna fata kocin Arsenal Mikel Arteta ya sake farfado da zawarcinsa kan matashin mai shekara 28. (Star)

Advertisement

Ɗan wasan Manchester City da Scotland mai buga tsakiya Caroline Weir, na gab da komawa Real Madrid a wannan kakar. (Telegraph – subscription required

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending