Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan wasan kwallon kafa: Makomar Kante, Dembele, Dybala, Di Maria, Gallagher, Perisic, Raphinha da kuma Gundogan

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

Advertisement

 

Manchester United na dubu yuwuwar zawarcin dan wasan Faransa N’Golo Kante, na Chelsea. (Guardian)

Advertisement

Liverpool ta tuntubi Ousmane Dembele, mai shekara 25, wanda kwantiraginsa da Barcelona zai kare a bazara. (Sport – in Spanish)

Kociyan Chelsea Thomas Tuchel zai tattauna da dan wasansa na tsakiya Conor Gallagher, mai shekara 22, kafin dan wasan na Ingila ya yanke shawara a kan makomarsa. Dan wasan ya shafe kakar da ta wuce a zaman aro a Crystal Palace. (Fabrizio Romano)

Advertisement

Conor Gallagher ya yi zaman aro a West Brom da Swansea City da kum Charlton Athletic

Wani dan wasan da shi ma zai tattauna makomarsa shi ne Ilkay Gundogan, na Manchester City, dan Jamus . (90min)

Advertisement

Wanda bisa ga dukkan alamu zai zama sabon kociyan Burnley, Vincent Kompany zai dauki Taylor Harwood-Bellis, mai shekara 20 dan wasansa na farko a zaman aro daga tsohuwar kungiyarsa Manchester City. (TSun)

Dan wasan Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 35, y ace an bar shi cikin bacin rai, kamar yadda ya rubuta wa Manchester United wata budaddiyar wasika, bayan da ya bar kungiyar. (Star)

Advertisement

Dan wasan gab ana gefe dan Croatia, Ivan Perisic, mai shekara 33, ya shirya kulla yarjejeniya da Tottenham Hotspur bayan da kwantiraginsa da Inter Milan ya kare. (Fabrizio Romano)

Kociyan Roma, Jose Mourinho na fatan doke tsoffin kungiyoyinsa Tottenham da Manchester United wajen zawarcin Paulo Dybala, dan Argentina mai shekara 28, idan kwantiraginsa ya kare da Juventus a bazaran na. (TyC Sports, via Express)

Advertisement

Paris St-Germain na matukar sha’awar daukar dan wasan gaba na Brazil Richarlison, mai shekara 25, daga Everton a bazaran nan. (Fichajes – in Spanish)

Mahaifin dan wasan gaba na gefe na Leeds Raphinha ya ce akwai yuwuwar dan wasan na Brazil mai shekara 25 ya je Barcelona, yayin da ake ta jita-jita kan labarin. (Express)

Advertisement

Juventus ta ba wa Angel di Maria, mai shekara 34, kwantiragin shekara daya bayan da ya bar PSG a karshen kakar nan. (Calciomercato – in Italian)

Dan bayan Manchester City, dan Japan Ko Itakura, mai shekara 25, na daukar hankalin Bournemouth da Fulham bayan ya taka rawar gani a zaman aron da ya yi a Schalke. (Sky Sports)

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending