Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Rudiger, Gnabry, Adeyemi, Mahrez, Milinkovic-Savic, Calvert-Lewin

Published

on

0 GettyImages 1210995196

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Newcastle United na sha’awar daukar dan bayan Jamus Antonio Rudiger, idan kwantiragin dan wasan mai shekara 29 ya kare da Chelsea a karshen kakar nan. (Telegraph)

Sai dai kuma Manchester United za ta yi gogayya da takwarar tata ta Premier a kan Rudiger a bazaran nan. (Express)

Advertisement

To amma matsalar da za ta iya samun United, a kokarin daukar dan bayan, ita ce rashin tabbas dangane da wanda zai karbi ragamar horas da kungiyar ta Old Trafford. (90min)

Watakila Arsenal ta nemi sake sayen dan wasan gefe na Jamus Serge Gnabry daga Bayern Munich, inda aka yi kiyasin darajar dan wasan mai shekara 26, da ya yi shekara hudu da Gunners ta kai fam miliyan 63. (Football.London)

Advertisement

Tottenham a shirye take ta saurari tayi daga kungiyoyin da ke son sayen dan wasanta na Brazil Emerson Royal, kasa da shekara daya da sayen dan bayan mai shekara 23, a kan fam miliyan 26 daga Barcelona. (Sun)

Tauraron dan gaban Borussia Dortmund na Norway Erling Braut Haaland yana son tafiya Barcelona a bazaran nan. (Sport – in Spanish)

Advertisement

Sai dai kuma shugaban Barcelona Joan Laporta, ya musanta rahotannin da ke cewa tuni ana shirin tattaunawa domin sayen Haaland, din wanda Manchester City da Real Madrid ke so. (Mail)

Dan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 28, ya gaya wa abokan wasansa cewa zai tsaya a Tottenham kaka mai zuwa idan har suka samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai kuma Antonio Conte ya zauna kungiyar. (Express)

Advertisement

Liverpool za ta samu damar sayen dan gaban Red Bull Salzburg dan Jamus Karim Adeyemi mai shekara 20 a lokacin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bazara, sai dai kuma kungiyar za ta iya fuskantar gogayya daga Borussia Dortmund. (Express)

Paris St-Germain da Chelsea na sha’awar sayen dan wasan Manchester City na Algeria, Riyad Mahrez, mai shekara 31. (Foot Mercato)

Advertisement

RB Leipzig ta bi sahun masu son sayen matashin dan bayan Real Madrid dan Sifaniya Rafa Marin mai shekara 19. (Marca – in Spanish)

Idan har Manchester United na son sayen dan wasan tsakiya na Serbia, Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27, daga Lazio, domin maye gurbin Paul Pogba ta sai ta fitar da yuro miliyan 80 ( fam 66m). (Sport Witness)

Advertisement

Tsohon dan wasan Arsenal Perry Groves ya shawarci kungiyar da ta nemi sayen dan wasan Everton na Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 24, a karshen kakar nan. (Star)

Everton za ta fuskanci matsalar biyan albashi idan har t fadi dag gasar Premier. (Mail)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending