Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Kante, Assensio, da Nunez, Calvert-Lewin, Schick
Daga kabiru basiru fulatan
Dan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26, ya shaida wa Leeds United cewa yana son ya rattaba hannu kan wata sabuwar kwantiragi a bazara, abin da ka iya sa masu sha’awar Manchester United, Liverpool, Newcastle, West Ham da Aston Villa suka ji kunya (Mirror)
Manchester United za ta iya amfani da dan wasan gaban Faransa Anthony Martial, mai shekara 26, a matsayin dan wasa a yarjejeniyar daukar kyaftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 28, daga Tottenham. (ESPN)
Manchester United ta shirya tsaf domin zawarcin dan wasan gaban Ingila Tammy Abraham, mai shekara 24, wanda ya ci wa kulob din Roma na Italiya kwallaye 23 a kakar wasa ta bana.
Everton za ta sayar da daya daga cikin tauraronsu na gaba, dan kasar Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 25, ko kuma dan kasar Brazil Richarlison, mai shekara 24, a bazara bayan ta yi asarar fan miliyan 121 a bara. (Sun)
Manchester United na zawarcin dan wasan gaban Benfica Darwin Nunez akan fam miliyan 60, amma fatansu na siyan dan wasan mai shekaru 22 dan kasar Uruguay ya danganta ne da samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (Telegraph subscription needed)
Newcastle United ta shirya tsaf don neman dan wasan bayan Bologna na Scotland Aaron Hickey, mai shekara 19, wanda za a ba shi damar barin kulob din na Italiya kan fan miliyan 15 zuwa 20. (Fabrizio Romano)
Babban marubucin wasan kwallon kafa na BBC Phil McNulty ya yi nazari kan yadda kocin Ingila Gareth Southgate ya kare Harry Maguire(Mail)
Dan wasan gefe na Netherlands Steven Bergwijn, mai shekara 24, ya yi nuni da cewa a shirye yake ya kawo karshen zamansa a Tottenham a wannan bazarar. (Mail)
Dan wasan gaba na Jamhuriyar Czech, mai shekara 26, Patrik Schick, wanda ake alakanta shi da komawa Arsenal ko Barcelona, ba zai bar Bayer Leverkusen ba, in ji shugaban kungiyar. (Goal)
Dan wasan tsakiya na Chelsea da Faransa N’Golo Kante, mai shekara 31, ya ki amincewa da bukatar Paris St-Germain a watan Janairu don ya koma zakarun na Faransa a bazara. (Le Parisien)
AC Milan na sake tunanin zawarcin dan wasan gaban Real Madrid Marco Asensio (Tuttosport)
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
