Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo : Makomar Rudiger, Assensio, Haaland, Lacazatte Pogba da Cavani

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

Manchester City ta kulla yarjejeniya da dan wasan Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21. (Mail)

Real Madrid ba ta son mayar da Haaland ɗan wasan da ya fi ɗukar albashi a ƙungiyar don ba ta son ta da zaune tsaye daga wajen ƴan wasanta. (Goal)

Advertisement

Idan yarjejeniyar Haaland ba ta cimma ruwa ba, Real za ta iya zawarcin dan wasan gaban Manchester United da Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 35, a maimakon haka. (Fichajes)

Real tana sa ido sosai kan dan wasan bayan Chelsea Reece James, mai shekara 22, manyan shugabannin kungiyar ciki har da Carlo Ancelotti sun kalli wasan dan wasan bayan na Ingila sau tara a kakar wasa ta bana. (Mirror)

Advertisement

West Ham United na tunanin dauko golan Ingila da Burnley Nick Pope, mai shekara 29 a bazara. (Times)

Lyon na daga cikin kungiyoyin da dan wasan gaba na Arsenal Alexandre Lacazette, mai shekara 30, ke tattaunawa da su game da komawarsa a bazara. (Canal Plus)

Advertisement

Juventus na son daukar Paul Pogba, mai shekara 29 a kyauta lokacin da kwantiraginsa na Manchester United zai kare a bazara, amma Bianconeri din za ta fuskanci hamayya mai zafi daga Paris St-Germain da Real Madrid kan dan wasan tsakiyar na Faransa. (Mediaset Sport)

Liverpool na zawarcin Serge Gnabry, mai shekara 26, a yanzu yana tattaunawa da Bayern Munich kan tsawaita kwantiragin. Kulob din na Bundesliga na sha’awar rike dan wasan na Jamus, wanda kwantiraginsa zai kare a shekara mai zuwa. (Goal)

Advertisement

Arsenal ce ke kan gaba wajen zawarcin dan wasan gaban Spain Marco Asensio na Real Madrid, da alama ita ma AC Milan na sha’awar ɗaukar dan wasan mai shekara 26(Calcio Mercato)

Newcastle na kan gaba wajen sayen matashin dan wasan Rangers mai shekaru 18 Alex Lowry bayan wakilin dan wasan tsakiyar na Scotland ya tattauna da shugaban daukar ma’aikata na Magpies. (Insider)

Advertisement

Manchester United da Erik ten Hag na gab da kammala tattaunawarsu amma za a jira sanar da yarjejeniyar a hukumance zuwa lokacin da za a cimma yarjejeniya kan biyansa diyyar Yuro miliyan 2 na jagorantar kungiyarsa ta Ajax. (Fabrizio Romano)

Real Madrid na duba yiwuwar siyan dan wasan bayan Chelsea Antonio Rudiger, mai shekara 29 a kyauta lokacin da kwantiraginsa zai kare a karshen watan Yuni.(ESPN)

Advertisement

Rudiger ya ki amincewa da Manchester United bayan sun tattauna da wakilansa. Abin da ya sa a gaba shi ne kulob din da ke da tabbacin samun tikitin shiga gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (Manchester Evening News)

Norwich City ta sake farfado da sha’awarta ta dauko dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Keinan Davis, mai shekara 24, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Nottingham Forest. (Insider)

Advertisement

Darektan wasanni na AS Monaco Paul Mitchell yana sa ido sosai daga masu sha’awar siyan Chelsea, wadanda ke ganin shi zai iya zama daraktan fasaha a Stamford Bridge. (The Athletic)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending