Connect with us

News

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Phillips, Haaland, Akanji, Rudiger, Araujo, Martinez, Fabiansk

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

Dan wasan Borussia Dortmund na Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21, zai yanke shawarar kungiyar da zai tafi nan da karshen watan nan na Afrilu, ko dai Real Madrid ko Barcelona ko kuma Manchester City a bazaran nan. (Sport – in Spanish)

Advertisement

Dan wasan da Manchester United ke harin dauka Manuel Akanji, mai shekara 26, yana son barin Borussia Dortmund kuma dan bayan na Switzerland na tunanin tafiya wata kungiya ta gasar Premier. (Sport1)

Barcelona ba ta da niyyar biyan kudin da Antonio Rudiger ke bukata, amma kuma kungiyar za ta sake ganawa da dan bayan na Jamus kan yadda za ta dauke shi idan kwantiraginsa ya kare da Chelsea a bazaran nan. (Sport – in Spanish)

Advertisement

Haka kuma Barcelonar tana son tattauna batun tsawaita zaman Ronald Araujo, wanda ya samu gayyata daga Manchester United, amma kuma dan bayan na Uruguay mai shekara 23, bai ji dadin zawarcin da Barcan ke yi wa Rudiger da dan bayan Denmark Andreas Christensen, shi ma na Chelsea ba. (Sport – in Spanish)

Arsenal da Tottenham na sha’awar Lautaro Martinez amma kuma Inter Milan ba za ta sayar da dan gaban dan Argentina mai shekara 24 ba, a kan farashin da bai wuce yuro miliyan 80 ba. (Calciomercato – in Italian)

Advertisement

West Ham za ta saka wa mai tsaron ragarta dan Poland Lukasz Fabianski, mai shekara 36, da sabon kwantiragi a kaka ta gaba. (Mail)

Aston Villa za ta yi kokarin tabbatar da ganin tafiya aron da Anwar El Ghazi ya yi kungiyar Everton ta kasance ta dindindin, a bazaran nan, to amma Everton din ba ta da niyyar rike dan gaban na gefe dan Holland mai shekara 26, idan lokacin aron nasa ya kare. (Football Insider)

Advertisement

Derby County ka iya samun farashi mai kyau a kan matashin mai tsaron ragarta Jack Thompson, mai shekara 15, ganin cewa Manchester City da Tottenham da kuma Chelsea, dukkanninsu na sha’awar matashin na Ingila. (Sun)

Birmingham City na shirin karbar tayi daga kungiyoyin Premier da wasu na Turai a kan matashin dan wasanta na tsakiya dan tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 18 George Hall, mai shekara 17. (Mail)

Advertisement

Newcastle na shirin gabatar da tayin fam miliyan 20 ga Brighton a kan mai tsaron ragar Sifaniya Robert Sanchez, mai shekar 24, a bazara, sannan kuma kungiyar tana harin sayen dan gaba na gefe na Watford dan Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 24. (Sun)

Everton za ta bar Allan ya tafi a bazara, duk da cewa dan wasan na tsakiya dan Brazil mai shekara 31, yana da sauran shekara daya a kwantirginsa. (Sun)

Advertisement

Aston Villa za ta nemi sayen dan wasan tsakiya na Leeds United dan Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26, fam miliyan 60 a bazaran nan. (Telegraph – subscription required)

Tsohon dan wasan tsakiya na Armenia Henrikh Mkhitaryan zai kasance ba shi da wani kwantiragi a kansa a bazara, to amma bayan da ya farfado da kwazonsa, a yanzu Roma za ta tattauna da dan wasan mai shekara 33 kan ba shi wani sabon kwantiragi a makon nan. (Fabrizio Romano on Twitter

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending