Connect with us

News

Buhari ba zai Iya kawo karshen matsalar tsaron Nageriya ba domin ta’addancin ya gama mamaye Gwamnatin sa ~Cewar Obasanjo.

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce rashin tsaro ya mamaye gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obasanjo na mayar da martani ne kan harin jirgin kasan Kaduna na baya-bayan nan inda aka ce mutane takwas sun mutu tare da jikkata da dama.

Advertisement

Ya yi magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin wani dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Dr Ugochukwu Williams, a gidansa na Penthouse da ke harabar dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, jihar Ogun.

A cewar Obasanjo, ’yan Najeriya da ke tafiya ba su da tsaro a kan hanya, a cikin jirgin kasa da kuma a filin jirgin sama

Advertisement

Ya kuma yi kira da a hada karfi da karfe domin dakile matsalar rashin tsaro a Najeriya, tare da yin takaici kan yadda lamarin ya mamaye gwamnatin Buhari.

Sai dai ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su bari halin da ake ciki ya mamaye kasar.

Advertisement

Ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya cewa yana da mafita kan kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta, don haka ne yake karbar duk wanda ya ziyarce shi da hannu biyu-biyu.

“Halin da mu ke a kasar nan, ba halin da mutum daya zai ce ya yi ba, yana da mafita, sai dai muna yaudarar kanmu. Na yi imanin cewa ya kamata mu zauna tare mu duba lamarin,” in ji

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending