Connect with us

Sports

Eden Hazard: Likitoci sun yi wa dan kwallon Belgium aiki kan raunin da yake fama

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

Advertisement

An yi wa Eden Hazard aiki a raunin da yake fama da jinya a Universitario Sanitas La Zarzuela, don tabbatar da dan kwallon ya warke gabaki daya.

Dakta Jose Palacios ne ya yi aikin tare da kulawar likitocin Real Madrid, kuma kawo yanzu Hazard yana gida, wanda ya fara jinya.

Advertisement

Mai shekara 31, wanda gwarzo ne a Premier League a Chelsea, na fama da jinya a kafarsa ta hadu karo da dama tun bayan da ya koma Real Madrid.

Har yanzu Real Madrid na fatan cin ribar kwarewar Hazard, kuma wannan aikin da likitoci suka yi masa zai kawo karshen jinya da yake yi a koda yaushe.

Advertisement

Hazard ya karya kafa a lokacin da yake buga wa Belgium tamaula a 2017, ciwon ya kara munana, bayan da takwaransa na Belgium, Thomas Meunier ya yi masa keta a gasar Champions League tsakanin Real Madrid da Paris Saint-Germain a Nuwambar 2019.

Bayan da Hazard ya murmure ya kara cin karo da koma baya a Fabrairun 2020, tun daga lokacin raunin ya hana dan kwallon sakat a harkar sana’arsa ta tamaula.

Advertisement

Hazard ya buga wa Real Madrid wasa 17 a kakar nan a La Liga a gasar da Real Madrid ke jan ragama da tazarar maki tara, duk da doke ta 4-0 da Barcelona ta yi.

Wasu rahotanni na cewar Hazard zai koma fagen tamaula nan da mako hudu ko biyar.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending