Connect with us

News

Najeriya za ta kashe naira biliyan uku wajen kwaso ‘yan ƙasar daga Ukraine

Published

on

1646232852805
Spread the love

Hamza Yusuf Abdulmumin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da kashe dala miliyan takwas da rabi – fiye da naira biliyan uku – wajen aikin kwashe ‘yan ƙasar daga ƙasashe huɗu maƙotan Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi a can.

Ma’aikatar harkokin waje da haɗin gwiwar ta agaji ne za su gudanar da aikin kwashe ‘yan ƙasar kusan 5,000 daga ƙasashen Poland da Ramania da Slovakia da Hungary.

Advertisement

Ƙaramin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya faɗa wa manema labarai a yau Laraba jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa cewa za a tura jirage uku don gudanar da aikin.

Jiragen sun ƙunshi na kamfanin Air Peace biyu da kuma na Max Air ɗaya.

Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen ta ce za a fara gudanar da aikin ɗebo su bayan sun tsallaka maƙota daga Ukraine sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin dakarun Rasha da na ƙasar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *