Labarai
Harin jirgin ƙasa: An yi shiru na minti 1 a taron mako-mako na FEC domin karrama fasinjojin da abin ya shafa

Daga kabiru basiru fulatan
Majalisar Zartaswa ta Tarayya, FEC, a yau Laraba a Abuja, ta yi shiru na minti ɗaya domin karrama waɗanda harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su.
Taron, wanda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, an fara shi ne da safiyar yau.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shine ya yi kira da a yi shiru na minti ɗaya domin karrama waɗanda abin ya shafa.
NAN ya ruwaito cewa jirgin kasan da ya taso zuwa Kaduna, ya bar Abuja da karfe 6 na yamma a ranar Litinin, inda wasu ‘yan ta’adda da su ka kai musu hari da misalin karfe 7.45 na dare, kusan mintuna 15 kafin isowa Kaduna.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
