Connect with us

News

Bayan El-Rufa’i ya zaɓi Uba Sani a matsayin Dan Takaran sa da zai Gwabza a Zaben fit da Gwani na APC

Published

on

Bayan El-Rufa’i ya zaɓi Uba Sani a matsayin Dan Takaran sa da zai Gwabza a Zaben fit da Gwani na APC

Ya umarce Dattijo ya janye Takara,

Advertisement

Hadiza ta jefar da tayin cigaba da riƙe Mataimakiya,
tace El-Rufai yakai Kasuwa.

Dattijo ya janye Takarar Gwamna, Hadiza tayi jifa da damar cigaba da zama Mataimakiya, bayan El-Rufa’i ya zaɓi Uba Sani a matsayin dan takaran sa

Advertisement

Sani Dattijo, tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jahar Kaduna ya sanar da janyewar sa akan ra’ayin sa na tsayawa Takarar Gwamna a Shekarar 2023, biyo bayan amincewa da Gwamnan yayi ma abokin hamayyar sa Uba Sani.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, Uba Sani wanda yake Wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijan Najeriya, shine Ɗan Takarar da maƙarraban Gwmanan suka zaɓa, dana kusan Gwamna, da Iyalai da kuma Ƴan Siyasar APC Gidan Gwabnatin Jahar Kaduna

Advertisement

A wani taron gaggawa na Masu ruwa da tsaki da Gwamna El-Rufa’i ya kirawo a ranar Laraba, Gwamnan ya gabatar da buƙatar zaɓar Ɗan Takara ta hanyar Sasanci, a gaban masu ruwa da tsaki na gidan Gwabna

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Mataimakiyar Gwamnan Jahar Hadiza Sabuwa Balarabe, da Sakataren Gwamnatin Jahar Balarabe Abbas Lawal, Shugaban Majalisar Dokoki Yusuf Zailani, da Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya Uba Sani, tsohon shugaban Ma’aikatar Gwamna, Sani Dattijo da sauran Yardaddun Masu ruwa da tsaki.

Advertisement

Wata Majiyoyi data halarci tattaunawar taron ya naƙalto Gwamnan yana cewa yaso mai gadon shi da Farko itace Mataimakiyar Gwamna Hadiza Balarabe, amma ya jefar da wannan tunanin, bayan ya tattauna da Shuwagabannin Addinai, dana Siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Gwamnan ya ƙara dacewa, tunda tikitin Hadiza Balarabe bazai iya tafiya a banza ba, to don haka ya zaɓi Mr Sani a matsayin Ɗan Takarar Gwamna daya zaɓa.

Advertisement

Gwamnan ya kuma yi wani canje-canje, inda ya bukaci Hadiza Balarabe ta cigaba a matsayin Abokiyar Takarar Uba Sani, damar da taƙi amincewa da’ita nan take.

Gwamnan ya kuma umarci Mr Dattijo daya canja Mazaɓa, ya nemi Sanatan Kaduna ta Tsakiya.

Advertisement

Waɗanda suka halarci taron sun ce Dattijo nan take yayi gaggawar amincewa da hukuncin Gwamnan cikin farin ciki.

A saƙon daya aike a Dandalin Gangamin yaƙin neman zaben sa, Matashi Dattijo yace ya amince da matsayar Gwamnan a matsayin abinda Allah ya ƙaddara, yana mai shan alwashin bada goyon baya ga Ɗan Takarar Sasanci domin samun nasarar shi.

Advertisement

“Salam, ina Son sanar daku, a taron daya wakana a ranar Laraba, Gwamnan ya umarce ni cewa muyi ruwa muyi tsaki, mu nemar wa Uba Sani goyon baya domin ya haye Kujerar Gwamna. Ya kuma umarce ni da in cigaba daga inda Uba Sani ya tsaya a matsayin Sanata mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya,” Saƙon Mr Dattijo.

“A yayinda wannan sakamako bashi muka tsara ba, ko muka so, amma mun amshe shi da ƙaddarawar Allah, wanda yake bada Mulki ga wanda yaso, a lokacin da yaso. A saboda haka, mun miƙa komai a gareshi, tare da addu’a ga Jaha dama Ƙasa data samu nagartattun Shuwagabanni a Shekarar 2023.

Advertisement

“Ina mai cigaba da godiya akan Jagorancin Mallam, da irin goyon bayan shi, wanda nake ɗaukar shi da mahimmanci. Na sayi Tikitin Tsayawa Takarar Gwamnan a APC, Amma zamu sayi na Sanata kamar yanda Allah ya Ƙaddara.

“Ina fatan zamu aiki a tare domin samun nasarar APC a dukkanin zaɓuɓɓukan. Goyon bayan ku, bamu ɗauke shi da wasa ba, kuma zamu cigaba da tunawa da godiya. Allah yabar zumunci.”

Advertisement

A yayinda muƙarraban Gwamnati suka amince da matsayar El-Rufa’i, amma har yanzu, Uba Sani zai je Zaben Primary da sauran Ƴan Takaran APC da suka haɗa da Manajin-Darakta na Hukumar NIMASA Bashir Jamo, da Alhaji Sani Shaaban Surukin Shugaban Kasa Bahari, dayace shi bai amince da hukuncin kama karya na Gwamna Nasuru El-Rufai ba sai an je an buga a Zaben Primary

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending