Connect with us

News

Kwastam ta kama sama da katan dubu uku na shinkafa ƴar waje a Kano da Jigawa

Published

on

Hukumar da ke yaƙi da fasa kwabri ta Najeriya wato kwastam ta kama sama da katan 3,387 na shinkafa ƴar waje da gwanjo da taliya da miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyaki da suka kai kusan naira biliyan biyu.

Advertisement

Jaridar Daily Trust a Najeriya ce ta ruwaito kwanturolan hukumar da ke kula da Kano da Jigawa MA Umar wanda ya sanar da kama kayayyakin a yayin wani taron manema labarai a Kano.

Ya bayyana cewa an kama kayayyakin ne tsakanin watan Maris zuwa Afrilun 2022 a jihohin biyu.

Advertisement

Ya kuma ce rundunar da yake jagoranta a cikin wata biyu ta samu ƙari a kuɗin shiga da take samu daga biliyan 9.6 zuwa biliyan 14 cikin watanni biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending