News
Siyasar Kano: Buhari ya tura jirgi Kano don ɗauko Shekarau
Daga yasir sani Abdullahi
Rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya na tabbatar da cewa shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya tura jirgi musamman jihar don ɗauko masa tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ya kai shi Abuja su gana.
Mai magana da yawun Malam Shekarau Sule Ya’u Sule, ya tabbatar wa BBC Hausa cewa cikin daren Juma’ar nan Shekarau ya karbi gayyatar shgaban ƙasar.
”Cikin daren nan Sardauna zai tafi Abuja, shugaban ƙasa ya turo yana nemansa, an turo jirgi ya ɗakko shi don tattaunawa da shugaban ƙasa da kuma iyayen jam’iyya” in ji shi.
Gabanin hakan an ga gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje wanda ke takun saƙa da Shekarau ɗin a gidan Sardauna, inda a nan ne ya sanar da shi gayyatar da shugaban ƙasar ya yi masa don sasanta su.
Sai dai mai magana da yawun Shekarau ɗin ya ce zuwa yanzu ba za su iya haƙiƙance ko shekarau zai amince da sulhu da ɓangaren Ganduje ba, har sai ya je ya gana da Shugaba Buhari, sannan an kammala tattaunawar da ake yi yanzu haka da magoya baya.
Rikici dai ya yi ƙamari tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Ganduje kan jagorancin jam’iyyar APC a jihar Kano, lamarin da ya kai ga har kotun ƙoli, daga bisani aka tabbatar da shugabancin jam’iyyar na ɓangaren Ganduje a matsayin halastacce.
An yi ta yaɗa rahotannin cewa tsohon gwamnan na Kano, Shekarau zai sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP ta Rabiu Musa Kwankwaso, kodayake Shekarau din bai bayyana haka da bakinsa ba.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama a Kano kamar tsohon mai ba wa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa Kawu Sumaila, da tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kabiru Alhassan Rurum da wasu yan majalisar dokokin jihar kusan 13 da na wakilai sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ta NNPP ta Kwankwaso.
