Connect with us

News

Karin Haske Akan Neman Takarar Sanatan Kaduna ta Arewa da Turadu Sha’aban ya fito a ADC

Published

on

IMG 20260510 WA0002

Ofishin Hon. Sani Muhammad Sha’aban ya bayyana cewa yunkurin Turadu Muhammad Sha’aban na neman takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Arewa a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ra’ayi ne na kansa, ba tare da sahalewa ko tuntubar iyalansa ba.

A wata sanarwa da sashin yada labarai na ofishin Hon. Sani Sha’aban ya fitar ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2026, an bayyana cewa Turadu, wanda ɗa ne ga Hon. Sani Sha’aban, ya dauki matakin neman takarar ne bisa ra’ayinsa, ba tare da neman shawara ko albarkar iyalansa ba.

Advertisement

Dangote Na Duba Yiwuwar Gina Sabuwar Matatar Mai A Kenya Mai Tace Ganga 650,000 A Kullum

Sanarwar ta ce an fitar da bayanin ne domin fayyace gaskiya tare da kaucewa duk wata fahimta mara kyau da ka iya tasowa a tsakanin jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.

Advertisement

“Muna sanar da jama’a cewa Hon. Sani Muhammad Sha’aban da daukacin iyalansa ba a sanar da su ba kuma ba a tuntube su ba kafin Turadu ya dauki wannan mataki,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa al’adar gidan Sha’aban ita ce duk da shekarun mutum ko matsayinsa, ya dace ɗa ya nemi shawara da albarkar iyayensa da iyalansa kafin ya shiga babban al’amari, musamman wanda ya shafi siyasa da shugabanci.

Advertisement

Sanarwar ta kuma jaddada cewa Hon. Sani Sha’aban har yanzu yana nan daram a jam’iyyar APC, yana kuma daga cikin ginshikan jam’iyyar tun daga matakin kasa zuwa jiha, yankin sanata, kananan hukumomi da ma mazabu.

A cewar sanarwar, Hon. Sha’aban ba shi da wata niyya ko shirin barin APC zuwa wata jam’iyya daban, inda ta bayyana cewa biyayyarsa ga jam’iyyar ta samo asali ne daga sadaukarwa, yakini da kuma kishin cigaban jam’iyyar da manufofinta.

Advertisement

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa Hon. Sha’aban na yi wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, addu’ar samun nasara a zaben shekarar 2027.

Kazalika, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga duk ɗan takarar da APC ta tsayar domin kujerar Sanatan Kaduna ta Arewa, tare da fatan dawowar Abbas Tajudeen a matsayin Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya a shekarar 2027.

Advertisement

Sanarwar ta ce Hon. Sani Sha’aban na goyon bayan duk wani abu da zai kawo cigaba, hadin kai da nasarar APC a Najeriya.

“Duk wanda ya san Hon. Sani Sha’aban ya san mutum ne mai cika alkawari, mai gaskiya da rikon amana, wanda ke tafiyar da rayuwarsa bisa ka’ida da manufa,” in ji sanarwar.

Advertisement

A karshe, ofishin ya bukaci jama’a da su fahimci karin hasken da aka yi dangane da batun neman takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Arewa da Turadu Sha’aban ke yi a karkashin jam’iyyar ADC.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending