News
Zaɓen Fidda-gwani: Tawagar kamfe ɗin Osinbajo ta ƙaryata labarin sama wa wakilan zaɓe 7,000 masauki
Daga yasir sani Abdullah
Ofishin Tawogar Yaɗa Labarai ta Kamfe ɗin Osinbajo ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta yi alƙawarin kama wa wakilan zaɓe na Jam’iyar APC 7,000 ɗakuna a otal-otal a yayin zaɓen fidda-gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Wacce rawa Gerrard zai iya takawa a wasansa da Man City don taimakawa Liverpool?
Tawagar yaɗa labarai, wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Alhamis a Abuja, ta buƙaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni.
“Mun ga wani labari mai tada hankali cewa wata ƙungiya mai suna Osinbajo Campaign Organisation ta ce za ta samar da masaukai ga wakilan jam’iyyar APC sama da 7,000 a fadin kasar nan a lokacin zaben fidda-gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
“Da yake danganta wannan ikirari ga Sanata Babafemi Ojudu, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman a ofishin mataimakin shugaban kasa, rahoton ya yi karyar cewa Ojudu ya sanar da hakan ga wakilai a Minna yayin da yake neman su zabi Osinbajo a lokacin zaben fidda-gwani na jam’iyyar.
“Gaskiya, Ojudu bai tabba yin irin wannan ikirarin ba kuma tawogar yakin neman zaben Osinbajo ba ta tanadi wannan tsari ba.
“Ya kamata a yi watsi da wannan rahoto na cewa za a bayar da masauki da abinci kyauta,” in ji ta.
Sanarwar ta ce mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da daukar lokaci yana tattaunawa kai tsaye da wakilan jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan tare da amsa tambayoyinsu kan harkokin siyasa da mulki.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
