Connect with us

News

Ƴan Najeriya sun kashe sama da naira biliyan 100 kan ilimi a ƙasashen waje cikin wata uku’

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Wata ƙididdiga daga Babban Bankin Najeriya wato CBN ta nuna cewa ƴan Najeriya sun kashe aƙalla dala miliyan 220.86 kan karatu a ƙasar waje daga Disambar 2021 zuwa Fabrairun 2022.

Shugaba Buhari ya isa Kano

Hakan na nufin sun kashe sama da naira biliyan 100 a kuɗin Najeriya.

Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito cewa CBN bai bayyana adadin da yan ƙasar suka kashe a watan Maris da Afrilu da Mayu ba, inda bankin ya ce akwai yiwuwar adadin da ya fitar na daga Disambar 2021 zuwa Janairun 2022 a samu sauyi.

Ɓangaren ilimi musamman na jami’o’i a Najeriya na cikin wani hali sakamakon irin yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending