Labarai
Zaɓar Atiku a matsayin mataimaki na ɗaya daga cikin kurakuren da na tafka s rayuwa ta — Obasanjo

Daga Kabiru basiru fulatan
Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ɗaya daga cikin kurakuran da ya tafka a rayuwarsa shi ne zaɓar mataimaki a 1999.
Gwamnoni 28 masu takarar sanata a zaɓen 2023
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar, shi ne ya yi wa Obasanjo mataimaki a lokacin da ya mulki ƙasar nan a tsarin demokradiyya daga 1999 zuwa 2007.
Da yake amsa tambayoyi a wani taro na wasu ɗalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun, kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito, Obasanjo ya ce “ba zan ce bana kuskure ba – Na yi su da yawa.”
“Amma wani abu da ya faru da ni shi ne Ubangiji bai taɓa kunyata ni ba. Kuma wannan abu ne mai muhimmanci.
“Misali, ɗaya daga cikin kurakuran da na yi shi ne ɗaukar mataimaki lokacin da zan zama shugaban ƙasa.
“Sakamakon wannan kuskure ne mai kyau, Ubangiji ya kare ni,” in ji Obasanjo.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
