News
Kotu Ta Ƙi Bayar Da Belin Matar Ike Ekweremadu a Birtaniya
Daga Mujahid danlami garba
Wata kotu a Birtaniya ta ƙi bayar da belin matar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu.
Mahara Sun Kashe Sojoji 30, Mobal 7, Farar Hula Da Dama
Kotun ta sanar da ƙin bayar da belin Beatrice mai shekara 55 ne a ranar Alhamis.
Ana tuhumar Beatrice tare da mijinta Sanata Ike Ekweremadu bisa zargin kai wani yaro kasar Birtaniya da zummar cire sannan jikinsa.
Beatrice ta bayyana a ɗakin shari’ar sanye da baƙar riga da wando.
Lauyanta ya shaida wa kotu cewa a yayin da ake tuhumar mijinta da haɗa baki wajen aikata laifin, wanda ke buƙatar amincewar atoni janar na ƙasar, ita tata tuhumar ba ta buƙatar sahhalewar atoni janar ɗin don ci gaban shari’ar.
A don haka ne ta shigar da buƙatar neman beli.
Sai dai lauyan da ya shigar da ƙara ya ƙi amincewa da belin, inda ya bayar da dalili da cewa akwai yiwuwar ta tsere idan aka ba ta belin, yana mai bayar da hujjojin da suka nuna hakan.
