News
Ana satar ganga 400,000 na ɗanyen fetur a kowace rana a Najeriya-Gwamnatin taraiya
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta koka akan yawan adadin ɗanyen man fetur da take asararsa daga sace shi, da ke kawo koma baya wajen samar da mai kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
Karamin minista na albarkatun man fetur na ƙasar Timipre Sylva, ne ya bayyana hakan a jiya a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma a fadar gwamnatin Jihar da ke Owerri.
Akwai ’Yan Kabilar Kanuri Sama Da Miliyan 2 A Kano’
Mista Sylva ya kara da cewa ɓata garin da ke aikata wannan laifi sun jawo adadin man da ake samarwa a rana ya ragu da wajen ganga 400,000, saboda haka a rana a maimakon a fitar da ganga miliyan 1.8 ya koma 1.4.
Sylva, ya samu rakiyar manyan kusoshin gwamnati da suka hada da ƙaramin ministan ilimi Goodluck Opiah, da babban hafsin jami’an tsaro Janar Lucky Irabo, da shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), da Alhaji Mele Kyari.
Ya bayyana zuwan nasu a matsayin babban yunkuri domin samar da dawamammar hanyar daƙile satar mai a Najeriya.
Ya kuma ƙara da cewa sun je jihar ne domin neman goyon bayan gwamnatin jihar wajen taƙalar matsalar.