News
Salman Rushdie ya farfaɗo bayan kai masa harin wuka a Amurka
Daga Kabiru Basiru Fulatan
Kafofin yada labaru a Amurka sun ruwaito cewar marubuci Salman Rushdie, wanda wani mutum ya caka ma wuka a wani taro a birnin New York, ya fara magana kuma an cire masa na’urar taimaka wa numfashi.
Sun ce wakilin marubucin Andrew Wylie ne ya tabbatar da hakan.
Tun bayan da aka kai Rushdie wani asibiti a Pennsylvania ne ranar Juma’a aka makala masa na’urar lumfashi sanadiyyar munanan raunuka da ya samu.
Mutumin da ake zargi da laifin caka wukar dai, Hadi Matar ya musanata tuhumar da ake masa na yunkurin kisan kai.
Shugaban Amurka Joe Biden ma ya shiga jerin mutanen da suka yi Allah-wadai da harin.
BBC news
Advertisements
