Connect with us

News

Kotu ta umurci matuƙan jiragen saman Kenya su koma aiki

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wata kotu a Nairobi ta umurci matuƙa jirgin saman Kenyan Airways su koma bakin aiki da ƙarfe shida na safen ranar Laraba, kuma su dakatar da yajin aikin da suka kwashe kwana huɗu suna yi.

 

Advertisement

Matuƙa jiragen saman sun shiga yajin aiki ne domin nuna adawa da matakin kamfanin jiragen na dakatar da kason da yake bayarwa ga asusun tara kuɗaɗen murabus na ma’aikata.

Kotu Ta Yanke Wa Dan Siyasar China Hukuncin Kisa Saboda Karbar Cin Hanci

Advertisement

Mai shari’a Anna Ngubuini Mwaure ta umurci matuƙan su koma bakin aiki har sai idan wata kotun ta yanke wani hukuncin da ya inganta matakin yajin aikin.

 

Advertisement

Ta kuma yanke hukuncin cewar kamfanin jiragen saman ya ƙyale matuƙa jiragen su yi ayyukansu ba tare da tsangwama ba.

 

Advertisement

Kamfanin dai ya ce yajin aikin na janyo masa hasarar kuɗi dala miliyan biyu da rabi a kowace rana.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending