Connect with us

News

A Naɗa Ministar Tsaro Mace A Ga Aiki Da Cikawa, Inji Ƴar Majalisar Wakilai

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

Ƙungiyar mata ƴan majalisa ta Najeriya ta yi kiran a naɗa mace a matsayin ministar tsaron Najeriya domin shawo kan matsalar tsaro.

Advertisement

 

Shugabar kwamitin majalisar wakilai kan mata Taiwo Oluga ce ta yi kiran ranar a lokacin taron ganawa da manema labaru a Abuja.

Advertisement

Kotu ta umurci matuƙan jiragen saman Kenya su koma aiki

Ta ce “Idan har aka naɗa mace a matsayin ministar tsaro, to kuwa za a ga aiki da cikawa, za ku ga sauyin da za a samu a ɓangaren tsaro.”

Advertisement

 

Ta nuna takaici kan yadda Najeriya ta kasance a baya-baya wajen shigar da mata a harkar gwamnati.

Advertisement

 

Ta ce bayanai na nuna cewa koda dukkanin matan da za su tsaya takara a Najeriya za su yi nasara, za a ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin mata a tafiyar da lamurran gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending