Connect with us

News

Wata Ɗalibar Jami’ar Nasarawa Ta Hallaka Kanta 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Wata ɗaliba ƴar aji ɗaya a Jami’ar Jihar Nasarawa (NSUK), Keffi, Mai suna Maikeffi Redemption Sarah, ta kashe kanta, ta hanyar shan guba.

Sarah, ƴar shekara 21, wacce ta kasance ita ce auta a gidan su an ce ta kashe kanta ne sakamakon tsananin damuwa.

Advertisement

Ba Za Mu Yarda Cin Hanci da Rashawa Ya Kara Ruguza Najeriya Ba – Hukumar EFCC

An sami rahoto cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a ɗakinta dake wajen makarantar a Unguwar Family and Friends Hotel daura da Jami’ar a Keffi.

 

Advertisement

Abokinta wanda shi ne ya wallafa labarin a shafin sa na Facebook, ya tabbatar wa jaridar Vanguard Faruwar lamarin ta wayar tarho.

 

Advertisement

“Na yi waya da ita a yammacin ranar Alhamis akan cewa za ta zo Akwanga daga Keffi, don halartar wani ɗaurin aure a a yau Asabar,Sai kawai jin labarin rasuwarta na yi.”

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ɗalibai da makwabta sun yi kokarin bata manja domin narkar da gabar amma abin ya ci tura.Tuni dai aka tafi da gawar marigayiyar ma’ajiya a garin Keffi.

Advertisement

Haka kuma wani ɗan uwan marigayiyar ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za a yi jana’izar ta a yau Asabar a garin su Akwanga.

A wani labarin kuma Ba Za Mu Yarda Cin Hanci da Rashawa Ya Kara Ruguza Najeriya Ba – Hukumar EFCC

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending